IQNA

Sallar Shiga Sabuwar Shekarar Noruz Ta Hijira Shamsiya A Tsakanin Kasashen Musulmi

Bangaren siyasa da zamantakewa: Bukin sallar shiga sabuwar shekarar hijira shamsiya ya fara yaduwa zuwa sauran kasasshen musulmi da kuma samun karbuwa a cikin al'adunsu.
Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; Said Muhammad Husein Ra'is zade shugaban ofishin yada al'adun Iran a kasar labanon a wata hira ta musamman da gidan Talbijin din Alkausar kan bukin sallar sabuwar shekara ta Iraniya hijira Shamsiya ya bayyana cewa: sallar noruz a yau ta samu karbuwa da kafuwa a cikin tarihi na tsawon lokaci kamar yadda wasu daga cikin masanma tarihi suka yi bayani kuma ta samo asali ne daga dubban shekaru da suka gabata da hakan ke nuni da matsayin wannan salla ta tunawa da shigar sabuwar shekara ta hijira shamsiya da kuma yadda ta samu karbuwa ko shakka babu a tsakanin kasashen musulmi.

380186