IQNA

Za A Bude Wata Tashar Kur'ani A Kan Tauraron Dan Adam A Gaza

15:25 - April 04, 2009
Lambar Labari: 1760084
Bangaren kasa da kasa: Ministan kula da harkokin addini na halastacciyar gwamnatin Palastinu karkashin jagorancin Hamas (Talib Abu shi'ir) ya bayyana cewa; za a bude wata tasahar talabijin da za ta rika watsa shirye-shiryen kur'ani daga Gaza a kan tauraron dan adam.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Nasij) cewa; Talib Abu Shi'ir ministan kula da harkokin addini na halastacciyar gwamnatin Palastinu karkashin jagorancin Hamas ya bayyana cewa; za a bude wata tasahar talabijin da za ta rika watsa shirye-shiryen kur'ani daga Gaza a kan tauraron dan adam. Kamar yadda ministan na Hamas ya nuna samfurin ayyukan da tashar za ta gudanar da zaran an bude ta, ya ce babbar manufar bude wannan tashar kur'ani ita ce yada koyarwa irin ta kur'ani mai tsarki. Daga cikin irin ayyukan tashar akwai shirye-shirye na karatu daga makarantan kur'ani, da kuma shirye-shiryen tafsiri gami da wasu shirye-shiryen na koyar da ka'idojin karatun kur'ani wato tajwidi, kamar yadda za a rika gayyatar manyan baki domin gabatar da bayanai masu amfani ga al'umma.


382140
captcha