Bangaren kasa da kasa: makarantar da kasuwanci a birnin rens na kasar Faransa na horar da talibai sanin tsarin banki a musulunci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga Grande Ecole sup de co Reims ta watsa rahoton cewa: wannan makaranta nada niyar koyar da tsarin banki na musulunci kuma tuni wannan makaranta ta kammala shirye-shiryen ganin hakan ta tabbata a nan bad a jimawa ba.Tuni talibai da dama suka yi maraba da wannan mataki mai kayatarwa matuka.
382102