IQNA

Ga Mai Bukata A Kasar Tanzaniya An Fassara Kur'ani Da Harshen Sawahiliya

13:39 - April 07, 2009
Lambar Labari: 1761549
Bangaren harkokin kur'ani: An fassara kur'ani da harshen Sawahili da kuma ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a Ketare ne ya dauki nauyin wannan aiki a kasar Tanzaniya ga mai bukata a wannan kasa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; tarjumar wannan kur'ani a cikin harshen Sawahili Sheik Ali Juma'a mayunga ne ya gudanar da wannan jan aiki na alheri kuma bi da yin gyara na karshe mu'assisar da ke kula da fassarar litattafai na Ansariyan da ke birnin Qum ta dauki nauyi da bugawa. Kofi dubu biyu ne na wannan fassara ofishin da ke kula da yada al'adun Iran ya sa a hannun wanda ya fassara domin rarrabawa ga mabukata a kasar Tanzaniya.Wannan tarjama ta hada da tafsirin Khulasar Tafsir na Sheik Mahmud Tehrani da harshe Sawahili.

383720
captcha