Bangaren al'adu da fasaha: An fassa littafin fikihu na jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Khameni a cikin harshen sawahili a kasar Tanzania.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an fassa littafin fikihu na jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Khameni a cikin harshen sawahili a kasar Tanzania. Daya daga cikin malaman cibiyar ilimi ta Hauza a birnin Dar salam na kasar Tanzania shi ne ya shiga gaba wajen gudanar da ayyukan fassarar. A can kasar Lababan ma an fassara wannan littafi na fikihu, wanda madaba'antar (alhadi) ta dauki nauyin fassarawa da bugawa. Littafin dai yana dauke ne da hukunce-hukuncen fikihu daidai da fatawar jagoran juyin juya halin Musulunci a kan mas'aloli na ibada, mu'amala da dai sauransu.
383704