Bangaren ilimi da nazari: A karon farako Mujallar Tamili a cikin Harshen Tudo a kasar seri Lanka ta fara bincike kan yancin addinai a Iran.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta kawo labarin cewa; Mujallar Tamili ta fara binciken sanin yancin da ake bawa addinai a Jmahuriyar musulunci ta Iran da kuma irin rawar da addinai ke takawa a wannan kasa musamma idan aka yi la'akari da makon hadin kai a tsakanin mazhabobin musulunci da ake gudanarwa a kowace shekara a kasar a daidai zagayowar ranar maulidi ta haifuwar fiyayyan halitta manzon rahama Muhammadu dan Abdullahi tsira da amincin Allah Ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka. Kuma sun yi la'akari da wasu litattafai kamar bayani kan rayuwar Fatimatul Zahra (AS) a matsayinta na abin koyi ga matan duniya musulmai.
384299