IQNA

Za A Fara Gyaran Cibiyoyin Addini A Arewacin Afganistan

Bangaren al'adu da zamantakewa: Kwamitin 'yan uwa musulmi na Afganistan gami da hadin gwiwar kwamitin malaman sunna da shi'a na lardin Balakh, sun fara rangadin duba cibiyoyin addini da ke arewacin kasar ta Afganistan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna reshen Afganistan ya habarta cewa; kwamitin 'yan uwa musulmi na Afganistan gami da hadin gwiwar kwamitin malaman sunna da shi'a na lardin Balakh, sun fara rangadin duba cibiyoyin addini da ke arewacin kasar ta Afganistan. Rahoton ya ci gaba da cewa mambobin kwamitocin biyu za su ci gaba da yin wannan rangadi domin gano cibiyoyin addini da ke yankin , tare da sanin matsalolinsu da kuma sanin abin da ya kamata a yi domin taimaka musu, kama daga gyransu idan suna bukatar gyara ko kuma sama musu da kayan aiki da dai sauransu. Daga cikin cibiyoyin da za su duba kuwa hard a makarantun addini da kuma masallatai, daga cikin masallatan kuma har da masallacin imam Hassan Mojtaba (AS) da ke lardin Marmal, inda 'yan sunna da kuma mabiya mazhabar shi'a suke gudanar da harkokinsu na addini baki daya.

384049