Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da taro kan ilimin sanin halayyar dan adam a mahangar addinin musulunci a kasar Tunusia.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (mohit) cewa; a ranar Alhamis da ta gabata ce aka fara gudanar da taro kan ilimin sanin halayyar dan adam a mahangar addinin musulunci a kasar Tunusia. Taron na samun halartar masana daga kasashe daban-daban domin bayyana mahangarsu kan yadda addinin musulunci yake kallon ilimin sanin halayyar dan adam. A wajen wannan taro ana gudanar da bincike a cikin littafai da dama da suke da dangantaka da wannan ilimi wannan malamai gami dam asana musulmi suka rubuta a zamunan da suka gabata da ma wadanda aka rubuta a wannan zamani, tare warware mahangarsu ko tabbatar da ita, daga cikin kasashen da suka tura masana dad a suka hada malaman jami'a domin halartar wannan taro, sun hada da Syria, Turkiya, Jamhuriyar musulunci ta Iran, Algeria, Masar, Kuwait, Bahrain, Morocco, da kuma Tunusia mai masafkin baki.
385682