Bangaren kasa da kasa:shirye-shiryen ofishin da ke kula da yada al'adun kasar Iran a Ketare a kasar Ghana a cikin watanni uku na farkon shekara ta hijira shamsiya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa labari kan ayyukan da ofishin kula da al'adun kasar Iran a ketare zai gudanar a cikin watanni uku na farkon shekara ta hijira shamsiya ta Iraniyawa.Daga cikinayyukan da zai gudanar akwai gudanar da tarorruka kan demokradiya a musulunci da jamhuriyar musulunci a Iran a matsayin abin koyi a sabuwa demokradiya ta musulunci kuma wannan tare da hadin guiwar kungiyar hadin kan musulmi kasar Ghana ne za a gudanar da shi.Sai kuma taron kan kaurar Imam Khomeini (R) da matsayin mace a musulunci.
387088