Bangaren fasaha: Baje kolin Iccen zaitun da aka saba gudanarwa a birnin Isfahan a bana za a gudanar a fadin kasar Iran.
Bayan ta nakalto daga bangaren hulda da jama'a na hadin guiwar kungiyoyin matasa masu shirya fina-finai ,cibiyar kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: ya zuwa yanzu an samu amsar masu bukata da dama da za su halarci wannan gurin baje koli da kuma sauran wadanda za a gudanar a fadin kasar ta Iran da kuma bayyana irin muhimmanci da hakan yake tattare da shi. Har ila yau ya kara da cewa bayan kasuwar baje kolin za a kuma gudanar da gasa a tsakanin mahalarta wannan kasuwar baje koli.
387466