Bangaren kasa da kasa: Taron kasa dakasa kan nazari a musulunci karo na biyu za a gudanar da shi a kasar Maleishiya a wannan shekara musamman a jami'a da ke lardin Salangur.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga majiyar labarai ta internert ta Pkukmweb cewa wannan taro za a gudanar da shi ne a kasar Maleishiya kuma shi ne irinsa karo na biyu da za a gudanar da zai yi nazari kan tunani da nazari a cikin musulunci da hakan yak e bawa masana da malummai da kuma masu bincike musulmi da wadanda ba musulmi ba damar yin nazari kan muhimman abubuwa a cikin wannan addini na musulunci da yake bawa kowa damar neman sani da bincike da ya shafi akida da bangarori na rayuwar dan adam .
389546