Bangaren zamantakewa: A yau ne aka gudanar da taron kasa na jinjinawa matasa da suka taka rawar gani a bangarori daban-daban na ci gaban kasa a fadin Iran da shugaban kasa Ahmadi Najad ya halarta.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta bayyana cewa; wannan taro da aka shirya da zummar girmama matasa da suka yi fice a fannonio daban daban na ci gaban kasa da al'umma a fadin Iran a girmama masu a babban dakin taro na gidan radiyo da talbijin na Iran tare da halartar shugaban kasar Iran ahmadiNajad wanda ya gabatar da jawabi mai gamsarwa matuka gaya da kuma yabawa matasa .Su mkansu matasan da suka karbi wannan kyautata ta girmamawa sun yaba da wannan taro da muhimmancinsa .
390676