IQNA

Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Za Ta Gudanar Da Zama Kan Palastinu

Bangaren kasa da kasa: Ministocin harkokin wajen kasashen larabawa za su gudanar da zamansu a birnin Alkahira na kasar Masar domin duba batun Qods da kuma halin da al'ummar palastinu suke ciki, gami da batun kai musu taimako.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Almujahid cewa; ministocin harkokin wajen kasashen larabawa na nan suna shirin gudanar da zamansu a birnin Alkahira na kasar Masar domin duba batun Qods da kuma halin da al'ummar palastinu suke ciki, gami da batun kai musu taimako. Sakataren kungiyar hadin kan kasashen larabawa shi ne ya sanar da hakan a wata zantawa da ta hada shi da manema labarai a birnin Alkahira, ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da taron ita ce tattauna batutuwa da suke da dangantaka da barazanar da masallacin Qods ke fuskanta daga yahudawan sahyuniya a cikin 'yan lokutan nan, da kuma batun aikewa da taimako ga al'ummar Gaza. Ya ce dole ne a samo hanyoyin taka wa Isra'ila birki kan ayyukan ta'addancin da take aikatawa kan al'ummar Palastinu da masallacin Qods.

391407