Bnagaren kasa da kasa: Wakilin kasar Niger a wajen taron alkalan kasashen musulmi da aka gudanar a birnin Tehran, ya bayyana cewa babban abin da ya baiwa Isra'ila dammar ci gaba da kasha musulmi a palastinu ba wani abu ba ne illa siyasar Majalisar Dinkin Duniya dangane da Isra'ila.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikan da wakilin kasar Niger a wajen taron alkalan kasashen musulmi da aka gudanar a birnin Tehran ya bayyana cewa; babban abin da ya baiwa Isra'ila dammar ci gaba da kasha musulmi a palastinu ba wani abu ba ne illa siyasar Majalisar Dinkin Duniya dangane da Isra'ila. Ya ci gaba da cewa kimanin shekaru satin ken an da Isra'ila ta mamaye yankunan palastinawa, amma har inda yau take ba a taba ganin Majalisar Dinkin Duniya ta dauki wani mataki na taka wa Isra'ila birki kan ayyukan ta'addancin da take tafkawa kan al'ummar palastinu ba, a kan haka ya ce nauyi day a rataya kan al'ummar musulmi da su baiwa 'yan uwansu goyon bayan da ya kamata, domin manufar Isra'ila it ace kawar da al'ummar muslmi da ma musulunci baki daya daga palastinu. Daga karshe ya ce dole ne a dauki dukkanin matakai na shari'a domin gurfanar da Isra'ila a gaban kotun manyan laifuka ta kasa da kasa dangane da ayyukan ta'addancin da ta aikata kan al'ummar Gaza.
393640