IQNA

Kungiyar Kare Hakkin Kananan Yara Ta Yi Suka Kan Yanayin Yara A Gaza

Bangaren kasa da kasa: Kungiyar lauyoyi masu kare hakkokin kananan yara ta kasa da kasa, ta yi kakkausar suka kan yanayin da kananan yara suka samu kansu a ciki a zirin Gaza, sakamakon hare-haren ta'addancin da Isra'ila ta kai kann al'ummar yankin, da kuma yadda yara suke fuskantar barazana a koda yaushe.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran SANA cewa; Kungiyar lauyoyi masu kare hakkokin kananan yara ta kasa da kasa, ta yi kakkausar suka kan yanayin da kananan yara suka samu kansu a ciki a zirin Gaza, sakamakon hare-haren ta'addancin da Isra'ila ta kai kann al'ummar yankin, da kuma yadda yara suke fuskantar barazana a koda yaushe.Rahoton ya ci gaba da cewa a cikin 'yan watannin da suka gabata bayan kisan kiyashin da kanan yara suka gani a Gaza, yanzu kuma ana ci gaba da matsa ma yara musamman ma 'yan kasa da shekaru goma sha uku, inda ha rake kam su tare yin awon gaba da su a cikin yankunan da ke gabar yamma da kogin Jordan, inda yanzu haka akwai daruruwan kananan yara da Isra'ila ta kame suke tsare a cikin gidan kasonta.

397710