Bangaren kasa da kasa; Tsohon gwamnan lardin Zikar na kasar Iraki Aziz Kazim Alawan ya bayyana cewa za a gina wata cibiya ta tattaunawa tsakanin addinai tare da kusanto da fahimtar juna a garin Nasiriya da ke cikin lardin Zikar a kudancin kasar Iraki.

Ya ci gaba da cewa birnin Nasiriyya birni ne mai tsohon tarihi, haka nan kuma akwai tsoffin gine-gine a cikinsa da suke komawa zuwa ga tarihin addinai musamman ma dai addinai wadanda aka safkar daga sama, a kan haka ya ce birnin nasiyya birni da ya dace a kafa wanna cibiya ta kasa da kasa ta tattaunawa tsakanin addinai a cikinsa, daga cikin wuraren tarihi da ke garin nasiriyya hard a wasu kufai da aka bayyana cewa gidan annabi Ibrahim AS ne a wurin.
399374