Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani zama na kasa da kasa a kasar yeman dangane da rawar da Musulunci ke takawa wajen gyara rayuwar al'umma ta zamantakewa a babban ginin cibiyar kula da al'adu da ilmomin addinin musulunci da ke birnin Taz a kasar Yeman.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar yeman saba cewa; An gudanar da wani zama na kasa da kasa a kasar yeman dangane da rawar da Musulunci ke takawa wajen gyara rayuwar al'umma ta zamantakewa a babban ginin cibiyar kula da al'adu da ilmomin addinin musulunci da ke birnin Taz a kasar Yeman. Shugaban cibiyar kula da al'adu da ilmomin addinin musulunci da ke birnin Taz na kasar Yeman Ahmad Abdulkarim Kubaisi ya bayyana cewa; an gudanar da wannan taron ne domin fito da wasu muhimman darussa da al'ummomi daban-daban za su iya dauka daga koyarwar kur'ani, wanda ya zo ma dan adam da mafificin tsarin rayuwa, kuma aiwatar da abin da ke cikinsa na tattare da tsirar al'ummomi.
399321