Bangaren siyasa: Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa ci gaba da yin gine-ginen majami'ar yahudawa da Haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a gefen masallacin Qods ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa, kuma ya zama wajibi a taka wa yahudawan sahyuniya birki dangane da keta alfarmar wurare masu tsarki da suke yi a birnin Qods.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; A wata zantawa da ta hada shi da manema labarai yau a birnin Tehran Hassan Kashkawi Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa ci gaba da yin gine-ginen majami'ar yahudawa da Haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi a gefen masallacin Qods ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa, kuma ya zama wajibi a taka wa yahudawan sahyuniya birki dangane da keta alfarmar wurare masu tsarki da suke yi a birnin Qods. Ya ci gaba da cewa abin da yahudawan sahyuniya suke aikatawa ba zai rasa nasaba da rashin daukar matakan da suka dace ban e daga bangaren musulmi, domin kuwa a cewarsa wajibi ne da ya rataya kan dukkanin gwamnatocin kasashen musulmi da su dauki kwararan matakai kan hakan amma abin takaici har yanzu babu wani abu da aka iya aiwatarwa.
399403