IQNA

An Fara Nuna Fim Din Tarihin Musulunci A Talabijin Din Jamus

Bangaren kasa da kasa: Gidan talabijin din zdf na kasar Jamus ya fara nuna fim din tarihin musulunci mai suna Mashrik, wanda ke bayani kan tarihin manzon Allah SAW da kuma bayyanar musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na gidan talabijin din Aljazeera cewa; Gidan talabijin din zdf na kasar Jamus ya fara nuna fim din tarihin musulunci mai suna Mashrik, wanda ke bayani kan tarihin manzon Allah SAW da kuma bayyanar musulunci.Rahoton ya ce wannan fin ya kunshi muhimman abubuwa da suka shafi sahihin tarihin musulunci da kuma irin gudunmawar da musulunci ya bayar wajen gina salihar al'umma da kyawawan dabi'u, kamar yadda fin yake nuna ilmomi da addinin musulunci ya kawo wadanda ci gaban dan adam ya dogara a kansu a halin yanzu, da kuma al'adun musulunci zamuna daban-daban, da kuma tasirin musulunci a tarihin nahiyar turai, musamman ma a kudanci da gabacin nahiyar. Wannan fim dai zai taimaka matuka wajen wayar da kan da dama daga cikin al'ummomin turai da ba su da cikakkiyar masani kan addinin musulunci da kuma koyarwarsa.

406927