Bangaren kasa da kasa: Manyan malaman birnin Najaf na kasar Iraki da ake komawa zuwa gare su sun fitar da bayanai a daidaiku kan rasuwar babban malamin addinin muslunci Ayatollah Muhammad Taki Bahjat, inda suka mika sakon ta'aziyya ga dukkanin al'ummar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Iraki na Barana cewa; Manyan malaman birnin Najaf na kasar Iraki da ake komawa zuwa gare su sun fitar da bayanai a daidaiku kan rasuwar babban malamin addinin muslunci Ayatollah Muhammad Taki Bahjat, inda suka mika sakon ta'aziyya ga dukkanin al'ummar musulmi. Daga cikin malaman da suka fitar da wananna bayani kuwa sun hada da Ayatollahu Ozma Sayyid Ali Sistani, Ayatollah Ozma Bashir Najafi, Ayatollah Ozma Ishaq Fayyadi, Ayatollah Ozama Sayyid Muhammad Sa'id hakim. A cikin bayanin Ayatollah sayyid Ali Sistani ya bayyana cewa; Rasuwar Ayatollah bahjat babbar asara ce ga duniyar musulmi, ya roki Allah day a gafarta masa ya yi masa rahama.
407702