IQNA

Bnagaren kasa da kasa: Wasu daga cikin manyan malaman addini na kasar Kuwait sun mika sakon ta'aziyya kan rasuwar Ayatollah Ozma Bahjat ga jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Al-dar ta kasar Kuwait cewa; Wasu daga cikin manyan malaman addini na kasar Kuwait da suka hada da Sheih Hossain Ma'atuk, da Ayatollah Muhammad Bakir Almuhri, sun mika sakon ta'aziyya kan rasuwar Ayatollah Ozma Bahjat ga jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei. A cikin bayanin manyan malaman sun bayyana rasuwar Ayatollah Ozma Bahjat da cewa wani babbar rashi ne ga duniyar musulmi da manyan cibiyoyin ilimi na Hauza. Sakon ya ci gaba da cewa Ayatollah Bahjat babban koyi ne ga dukkanin musulmi ta fuskacin tsoron Allah da kyawan dabi'u da koyi da iyalan gidan manzon Allah SAW, kamar yadda ya kasance babban kogi na ilimi da irfani da gudun duniya.

407780