IQNA

Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da wata gasa ta kasa da kasa a palastinu dangane da nazari kan ilmomin addinin musulunci a fagage daban-daban a karkashin kulawar cibiyar kula da harkokin nazari da bincike kan addinin musulunci ta palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran palastinu wafa cewa; : Za a gudanar da wata gasa ta kasa da kasa a palastinu dangane da nazari kan ilmomin addinin musulunci a fagage daban-daban a karkashin kulawar cibiyar kula da harkokin nazari da bincike kan addinin musulunci ta palastinu. Ministan kula da harkokin addinin muslunci na palastinu Talib Abu Shi'ir ya bayyana cewa; masu gudanar da bincike kan addinin musulunci za su iya yin nazari musamman kan rayuwar ma'aiki SAW da kyawawan dabi'unsa da kuma matsayinsa a cikin al'ummar musulmi da ma ta fuskacin 'yan adamtakarsa, ta yadda hakan zai bas u damar gane cewa addinin musulunci addini ne na zaman lafiya da sulhu da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai.

408260