Bangaren siyasa da zamantakewa: Za gudanar da taro a kasar Maleishiya kan nazarin tasirin tunanin Imam Khomeini kan hadin kan musulmi da ofishin da ke kula da yada al'adun Iran ne ya dauki dawainiyar gudanarwa>
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: wannan taro zai yi dubi da bayani ne kan yadda wannan tunani da hangen nesa na Imam Khomeini ® wanda ya assasa jamhuriyar musulunci a Iran ya kaddamar da wannan hanya ta samara da makon hadin kai a tsakanin musulmi da yadda musulmi daga kasashe daban-daban masana da malummansu da kuma marubuta da sauran bangarori na al'umma ke rayuwa kuma wannan taro zai yi dubi kan yadda wannan tunani ya taimaka wajen kara kusancin musulmi da hada kansu a duniyar musulmi.
408220