IQNA

15:37 - May 24, 2009
Lambar Labari: 1782431
Bangaren kasa da kasa: A lokacin da mai tafsirin kur'ani ke yin amfani da ayoyin kur'ani masu yawa wajen fassara wata aya daga cikin ayoyin kur'ani dangane da wani maudu'I guda, domin hada ma'anar ayar ta yadda zata bayar da cikakkiyar ma'anarta, yana bukatar ruwayoyi da hadisan ahlul bait domin tabbatar da cikakkiyar da ayar ke nufi ba tare da samun wata karkata ba.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga tashar talabijin Rasid cewa; a cikin wani bayani da marubucin nan na kasar Saudiyya Mahmud Musawi ya yi dangane da tafsir Maudu'I ya bayyana cewa; A lokacin da mai tafsirin kur'ani ke yin amfani da ayoyin kur'ani masu yawa wajen fassara wata aya daga cikin ayoyin kur'ani dangane da wani maudu'I guda, domin hada ma'anar ayar ta yadda zata bayar da cikakkiyar ma'anarta, yana bukatar ruwayoyi da hadisan ahlul bait domin tabbatar da cikakkiyar da ayar ke nufi ba tare da samun wata karkata ba. Ya ci gaba da cewa a cikin littafin da ya rubuta kan tafsir maudu'i ya yi kokari ya fassa wasu ayoyi da wasu ayoyin, amma ta hanyar yin la'akari da haduwar ma'ana da kuma dalilan safkar ayoyin, gami da hadisan manzon Allah da ahlul baiti da suka yi Magana kan ayoyin da kuma ma'anoninsu, ta yadda ma'anar za ta yi daidai da abin da ayoyin suka kunsa na ma'ana.


409498
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: