Bangare kasa da kasa: Jami'ar Azzahar dake kasar Masar ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta bukaci kyautata salon koyarwa a Yammacin Turai domin haskaka fuskar musulunci a turan.
Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ce ta bayyana wannan labari bayan ta nakalto daga jaridar kasar Masar ta Akhbar cewa; Mustapha Haluji malami mai karantar da koyarwar kur'ani a jami'ar Azzahar da ke birnin Alkahira ya nuna farin cikinsa da wannan shiri da salo da zai taimaka wajen ganin an cimma manufar abin da ake son cimma ta yadda addinin musulunci ta hanyar da ta dace da haskaka matsayin musulmi da musulunci a nahiyar Turai.
409363