IQNA

16:35 - May 26, 2009
Lambar Labari: 1783473
Bangaren kasa da kasa: A jiya ne aka gudanar da taron nuna cikakken goyon baya ga masallacin Qods mai alfarma a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda ya zo daidai da lokacin zabar birnin ya zama babban birnin al'adu na kasashen larabawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na arab news cewa; A jiya ne aka gudanar da taron nuna cikakken goyon baya ga masallacin Qods mai alfarma a birnin Aman fadar mulkin kasar Jordan, wanda ya zo daidai da lokacin zabar birnin ya zama babban birnin al'adu na kasashen larabawa. Rahoton ya ci gaba da cewa wannan taro ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen larabawa da ma na musulmi, musamman ma jami'ai daga bangarorin kula da al'adu da na siyasa. Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabansu a wurin taron hard a limamin masallacin Qods Haj Zaki Algol, wanda ya bayyana cewa babbar manufar yahudawan sahyuniya kan ci gaba da yin gine-gine a cikin masallacin Qods ita ce kawar da duk wata alama ta musulunci da ke cikin birnin mai alfarma.


410770

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: