IQNA

An Bude Baje Kolin Kayayyakin Tarihin Musulunci A Norway

Bangaren kasa da kasa: A jiya ne aka bude baje kolin kayayyakin tarihin musulunci a cibiyar kula da harkokin musulunci da ke birnin Auslo fadar mulkin kasar Norway.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Alwatan ta kasar Saudiyya cewa; A jiya ne aka bude baje kolin kayayyakin tarihin musulunci a cibiyar kula da harkokin musulunci da ke birnin Auslo fadar mulkin kasar Norway. A lokacin da ake gudanar da taron bude wannan baje koli sarauniyar kasar Norway da wasu daga cikin shugabannin musulmi da kuma jami'ai a bangaren harkokin al'adu na kasar duk sun samu halartar bukin bude baje kolin. Wasu daga cikin jam'iyun siyasa na kasar Norway masu tsattsauran ra'ayi da tsananin gaba da musulunci, da kuma wasu kungiyoyin yahudawa na kasar sun yi kakkausar suka dangane da halartar sarauniya Soniya ta kasar wajen bukin bude wannan baje koli.

412742