Bangaren ilimi da fikira; Za fara gudanar da wani zaman tattaunawa tsakanin addinai da aka safkar daga sama a kasar Crotia, da nufin samun fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da za a gudanar da irin wannan zama.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Za fara gudanar da wani zaman tattaunawa tsakanin addinai da aka safkar daga sama a kasar Crotia, da nufin samun fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da za a gudanar da irin wannan zama. Bayanin ya ci gaba da cewa bangaren kula da harkokin al'adu na ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran da ke babban birnin kasar Crotia tare da hadin gwiwa tare da cibiyar raya al'adun musulunci ta kasar sun e suka shirya gudanar da wannan zaman tattaunawa tsakanin mabiya addinai da aka safkar daga sama, da nufin kara samara da fahimta tsakanin mabiya addinan. Shugaban bangaren kula da harkokin al'adu na ofishin jakadancin Iran ya bayyana cewa taron zai samu halartar wasu daga ciki masana na kasar da kuma jagororin addinai.
414480