Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin sana cewa; An zaman tattaunawa tsakanin addinai da al'adu na kasa da kasa da aka gudanar a birnin Kirwan na kasar Tunisia, wanda majalisar dinkin duniya ta dauki nauyin shiryawa. Mahalarta taron da suka fito daga kasashen duniya daban-daban sun jaddada wajabcin fahimtar juna tsakanin dukkanin addinai da al'adu na duniya, tare da zama da juna lafiya cikin sulhu ba tare da samun rikice-rikice ba. Tawagar Iran da ta halarci zaman taron, ta taka rawa wajen tabbatar da fahimtar juna tsakanin mahalarta taron taro wadanda sun fit one daga kasashen duniya daban-daban da kuma mabanbanta ra'ayoyi na addini da al'adu.
416291