IQNA

An Fitar Da Wani Littafi Dangane Da Zaman Jahiliyya A Cikin Kur'ani

Bangaren adabi; An fitar da wani littafi da yake Karin haske dangane da zaman jahiliyar larabawa a cikin kur'ani mai tsarki, wanda wata marubuciya 'yar kasar Iraki mai suna Ansiya Khazali ta rubuta.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An fitar da wani littafi da yake Karin haske dangane da zaman jahiliyar larabawa a cikin kur'ani mai tsarki, wanda wata marubuciya 'yar kasar Iraki mai suna Ansiya Khazali ta rubuta. A bangare guda kuma an kaddamar da wani shiri na na kur'ani da zai taimaka a zamannace wajen sanin ilimimomin kur'ani, wanda cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci da ayyukan alkhairi ta kasar ta dauki nauyin gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa shugaban cibiyar kula da harkokin kur'ani na kasar ya bayyana cewa; wannan shirin yana dauke da alfanu ga dukkanin musulmi, musamman ma ma'abuta kur'ani daga cikinsu, domin kuwa wannan shiri zai taimaka wajen sanin dukkanin harkokin da ake gudanarwa a duniyar musulmi da suka shafi kur'ani mai tsarki.

418358