IQNA

Kisan Marwah Sharbini Abin Kunya Ne Ga 'Yan Adamtaka

15:43 - July 15, 2009
Lambar Labari: 1802167
Bangaren siyasada zamantakewa; Daya daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar Labanan daga bangaren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah Hussain Musawi ya bayyana cewa kisan gillan da aka yi wa Marwa Sharbini a kasar Jamus abin kunya ne ga 'yan adam baki daya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na ofishin 'yan majalisar dokokin kasar Labanan cewa; Daya daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar Labanan daga bangaren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah Hussain Musawi ya bayyana cewa kisan gillan da aka yi wa Marwa Sharbini a kasar Jamus abin kunya ne ga 'yan adam baki daya. Bayanin ya ci gaba da cewa babban abin kunya ne ta fuskoki da dama, da hakan ya hada da cewa an kasha wannan matar neb a tare da ta sabawa ko daya daga cikin dokokin kasar Jamus ba, bat a saba dokar wata kasa ba, bat a saba ma wani mutum ba, ba ta ci mutuncin kowa, amma kuma an kasha ta a cikin kotu da ke raya kare hakkin dan adam, a gaban jami'an tsaron daya daga cikin manyan kasashen tarayyar turai.

433095



captcha