Bangaren fikira da ilimi; Minista mai kula da harkokin ilimi na kasar Afganistan ya bayyana cewa an sake bude wasu manyan makarantu uku da 'yan kungiyar Taliban suka rufe a garin Gizni na kasar a lokutan baya, kuma za a ci gaba da gunar da harkoki na koyar da karatu a cikin su kamar yadda aka saba a lokutan baya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga reshensa da ke kasar Afganistan cewa; Minista mai kula da harkokin ilimi na kasar Afganistan ya bayyana cewa an sake bude wasu manyan makarantu uku da 'yan kungiyar Taliban suka rufe a garin Gizni na kasar a lokutan baya, kuma za a ci gaba da gunar da harkoki na koyar da karatu a cikin su kamar yadda aka saba a lokutan baya. Bayanin ya ci gaba da cewa tun lokacin da mayakan Taliban suka rufe wadannan makarantun addini ba a sake gudanar da karatu ko wasu harkokin addini a cikinsu ba, amma daga inda yau take an bude, makarantun kuma za a ci gaba da gudanar da dukkanin harkoki a cikinsu kamar lokutan baya.
434963