IQNA

Taron Gasar Karatun Kur'ani A Iran Ta Kayatar Da Mahalarta

10:34 - July 23, 2009
Lambar Labari: 1804603
Bangaren kasa da kasa; Taron gasar karatun kur'ani da ke gudana a birnin Tehran ya kayatar da dukkanin mahalarta gasar.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga bangaren yada labaransa dake halartar gasar karatun kur'ani daga bangaren yada labarai na kwamitin da ke kula gasar cewa; Taron gasar karatun kur'ani da ke gudana a birnin Tehran ya kayatar da dukkanin mahalarta gasar, inda suka bayyana tad a cewa tana tattare da ruhin hadin kai tsakanin musulmi mabiya mazhabobi daban-daban na musulunci da suka zo Iran domin girmama kur'ani mai tsarki da daukaka kalmar Allah. Bayanin ya ci gaba da cewa taron gasar wanda yake samun halartar daruruwan makaranta daga sassa daban-daban na kasashen duniya, musamman ma daga kasashen musulmi, wadanda suke halartar tarukan gasar karatun kur'ani da ake gudanarwa a sassa daban-daban na duniya.
436704

captcha