IQNA

14:54 - July 23, 2009
Lambar Labari: 1805090
Bangaren kasa da kasa; An tura wasu daga cikin daliban jami'a na kasar Kuwait zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da ayyukan zira da kuma Karin ilmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait cewa; Minista mi kula da harkokin addinin musulunci a kasar Kuwait a wata zantawa da ta hada shi da manema labarai a yammacin jiya a birnin Kuwait ya bayyana cewa; An tura wasu daga cikin daliban jami'a na kasar Kuwait zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da ayyukan zira da kuma Karin ilmi, wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar Kuwait ce ta shirya wannan tafiya tare da daukar nauyin dukkanin daliban da suke wannan tawaga.
Ya ci gaba da cewa wanna tafiya tana da matukar muhimamnci ga daliban musamman wadanda suke bincike kan wasu abubuwa da suka dangaci tarihin musulunci.
437376
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: