IQNA

Masu Gaba Da Musulunci Danmark Na Ci Gaba Da Tsananta Sukar Musulmi

14:53 - July 23, 2009
Lambar Labari: 1805092
Bangaren kasa da kasa; jam'iyar masu adawa da addinin musulunci a kasar Danmark ta bukaci da a kori wata musulma a cikin runduranar sojin kasar, sakamakon saka dan kwali da take yi a kanta, wanda hakan ke nuni da alamar musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran dunya bulteni cewa; jam'iyar masu adawa da addinin musulunci a kasar Danmark ta bukaci da a kori wata musulma a cikin runduranar sojin kasar, sakamakon saka dan kwali da take yi a kanta, wanda hakan ke nuni da alamar musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ba shi ne karon farko da masu tsananin gaba da addinin musulunci a kasar danmark suke bukaci da a dauki matakan takura mabiya addinin musulunci a kasar ba. Duk da cewa babu wata ayar doka a cikin kundin tsarin mulkin kasar Danmark da ta hana dakarun kasar mata saka dankwali, amma matsin lamabar masu tsananin gaba da addinin muslunci ya sanya rundunar sojin kasar kiran matar domin yi mata tambayoyi, wanda wata kila hakan ya sa a koreta.
437398
captcha