Abdulkadir Shahid Uglu fitacce kuma mahardacin kur'ani dan kasar Turkiya kuma daya daga cikin alkalan da suka yi alkalanci a gasar karatun kur'ani a Tehran a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ya bayyana cewa; yana bada shawara ga alkalan da aka zaba su bada daraja ga makaranta da su kaucewa bawa yan kasarsu makin dab a su cancanta misali a lokacin da mai harda daga kasar Turkiya ya kamala karatu ban ba shi maki ba amma sauran ba haka suka yi da yan kasarsu sai ma suka fifita su.
437981