IQNA

Bangaren Zamantakewa: Zama na musamman kan nazarin yin azumi a mahangar addinan Allah.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa;wannan zaman taro da bincike za a yi shi ne karkashin halartar masana da kwararru kan harkokin addini da za yi nazari kan muhimmanci da matsayin yin azumi a tsakanin addinai na Allah kuma za su kwatamta wannan takalifi da wajibci da Allah ya wajabtawa mabiya addinai.

463452