Kamfanin dillancin labran Iqna ya nakalto daga shafin internet na sautul Irak cewa; An girmama wadanda suka udanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a kasar Austaralia, wadda aka yi wa lakabi da gasar Imamul Muntazar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasa ta samu halartaar musulmi mazauna kasar, wadanda suka fito daga kasashen musulmi da na larabawa daban-daban. Musulmi dai su ne marassa rinjaye a kasar Austaralia, kuma suna gudanar da dukkanin harkokin addininsu duk da mtsallin da suke fuskanta a wasu lokuta daga masu tsattsauran ra'ayin kiyayya da Musulunci. 467494