Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wannan arangama ta zo ne a daidai lokacin da ‘yan kungiyar ‘yan uwa musulmi da kuma masu adawa da su suka fito domin tunawa da ranar 6 ga watan Oktoban shekara ta 1973, inda Masar ta samu nasara a yakin da ta gwabza ga haramtacciyar kasar Isra’ila, wanda kuma ya zama shi ne yaki na karshe tsakanin Masar da Isra’ila.
A nata bangare ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Masar ta ce an kame wasu mutane dauke da makamai a yayin dauki ba dadin na a wasu yankuna na kasar Masar, bayanin ya ce akasarin mutanen da aka samu da makaman magoya bayan kungiyar ‘yan uwa musulmi ne, amma kungiyar ba ta kore ko tabbatar da wannan bayani ba.
Wasu rahotannin kuam sun ce Jami'an tsaro a kasar Masar sun kashe Mutane biyu a yankin Kalyubiya dake arewacin kasar Shugaban 'yan na wannan yanki Mahmud Yasri ya bayyana cewa wasu Mutane dauke da makamai suka shiga gidajen jirkan kasa mai jgilar al'ummar kasar a anguwar Amal dake wannan yaki inda suke kokarin kai hari a cikin wannan Jirki.
Bayan da Jami'an tsaro suka samu labarinsu sun kai sumame inda suka kashe Mutane biyu sannan suka kama Mutane biyar tare da jikkata wani adadi mai yawa daga cikinsu, jami'in ya ci gaba da cewa jami'an tsaro na ci gaba da farautar wasu Mutanan wadanda ake zarki suna hadin bakin da wadannan Mutane kan kokarin da suke na kai wannan hari.
A gumurzun jiya juma'a ma tsakanin magoya bayan hambararen shugaban kasa Muhamad Mursi da jami'an tsaro kimanin Mutane 4 ne suka rasa rayukansu sannan fiye da Mutane 40 suka samu mummunan rauni.
Jami'an tsaro sun karfafa matakan tsaro a wasu manyan hanyoyi na kasar saboda abinda ya faru a jiya juma'a har ila yau wasu bayanai na nuni da cewa jami'an tsaro sun kewaye dandalin Tahrir tare da wasu manyan hanyoyi masu zuwa fadar shugaban kasar na Masar har sai ranar litinin mai zuwa.
1298820