Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jim kadan bayan fitar da wannan hukunci, jami’an tsaro sun ci gaba da kame manyan jagororin kungiyar, mutum na bayan nan da aka kama dai shi ne Salahuddin Abdulhalim Sultan, wanda ya taka gagarumar rawa wajen jagorantar Zanga-zangar nuna kin amincewa da kifar da gwamantin Muhammadu Mursi.
To daga Masar bari mu leka Guinea Conakry, inda a kalla mutum guda ya rasa ransa a taho mu gama tsakanin magoya bayan gwamnatin kasar da kuma ‘yan hamayyar siyasa. Raotannin daga kasar sun ce an yi taho mu gama ne a tsakanin masu yakin neman zabe na jam’iyyar da ke mulki a kasar da kuma sauran jam’iyyun adawa na siyasa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutum guda tare da jikkatar wasu 51.
Kwamitin lauyoyin kungiyar Ihwanul-Muslimin ta Muslim Brotherhood ta kasar Masar ya mai da martani kan hukuncin da wata kotun Masar ta fitar kan haramcin kungiyar a jiya Litinin.
Kwamitin lauyoyin kungiyar Ihwanul-Mulimin ta kasar Masar a jiya Litinin ya sanar da cewar hukuncin da wata kotun kasar ta fitar kan rusa kungiyar, hukunci ne da baya kan doka, kuma kotun ba ta da hurumin daukan irin wannan mataki kan kungiyar.
Har ila yau Baha’u Abdur-Rahman daya daga cikin mambobin kwamitin lauyoyin kungiyar ‘yan uwa musulmi ta kasar Masar ya bayyana cewar lauyoyin kungiyar Ihwanul-Muslimin sun shirya daukan matakan kalubalantar wannan hukunci tare da binciken dalilan da suka janyo fitar da shi.
A jiya Litinin ne wata kotu a birnin Alkahira na kasar Masar ta fitar da hukuncin hana gudanar da duk wasu ayyukan kungiyar Ihwanul-Muslimin tare da bada umurnin kwace dukiyoyin kungiyar da na mambobinta.
1293709