Bangaren kasa da kasa: za a gudanar da kasuwar baje kolin tarihin gwagwarmaya ta al'ummar Palasdinu inda za a yi bayani kan munanan ayyukan Yahudawan Sahyoniya kan Palsdinawa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga Sana ta watsa rahoton cewa: Jamal Muhsin komandan Nablus a cikin wani bayani day a gabatar ya bayyana cewa: wannan kasuwar baje koli za a samu halartar daruruwan dubban mutane Palsdinawa domin nuna yadda suke tare da al'ummar Palsdini da kuma yadda al'adu da wayewa ta hada su tare da jaddada cewa: ci gaba da gwagwarmaya har sai sun samar da ynacin yankunan Palsdinu da kawo karshen wannan mamaye na yahudawan sahayoniya yan babakere. Har iya Ziyad Usman kakakin komandan Nablus din a wata hira da manema labarai ya bayyana cewa: dukan mu'assisoshi na al'umma da shugabannin Palasdinawa da mambobin komitin al'umma da wakilan jam'isu da kungiyoyi daban-daban na musulmi suna daga cikin wadanda za su halarci wannan gurin baje kolin wannan kasuwa.
489623