IQNA

Ana Bincike A Kasar Garkijistan Kan Rawar Da Addinai Ke Takawa Wajen Yaki Da Ta'addanci

Bangaren ilimi: Ana Bincike A Kasar Garkijistan Kan Rawar Da Addinai Ke Takawa Wajen Yaki Da Ta'addanci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; a wajen wannan zama da cibiyar da ke kula da yada al'adun Iran a wannan kasa ta Garkijistan ta shirya zai samar da wata hanya ta tattaunawa tsakanin addinai da samar da kusanci a tsakanin mazhabobi na Musulunci da jami'o'I na addinai da muassishoshi na Ahli Baiti (AS) a wannan kasa ta Garjistan. Har ila yau a gurin wannan taro an karanto jawabin Ayatullahi Muhammad Ali Taskhiri babban sakataren kungiyar kara kusanci a tsakanin mazhabobi day a bayani kan muhimmancin gudanar da irin wannan taro.

531667