Bangaren kasa da kasa Muhammad Said Dandawi Sheikh Azhar a wajajen karshen rayuwarsa a wata ganawa da Shimon Perez shugaban Haramtacciyar kasar Isra'ila ya fuskanci suka da fushin al'ummar musulmin duniya bayan da ya nuna mashru'iyar gina katangar zalunci ta haramatacciyar kasar Isra'ila da killace Palasdinawa cikin yunwa da duhu hali ne.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa; Muhammad Said Dandawi Sheikh Azhar a wajajen karshen rayuwarsa a wata ganawa da Shimon Perez shugaban Haramtacciyar kasar Isra'ila ya fuskanci suka da fushin al'ummar musulmin duniya bayan da ya nuna mashru'iyar gina katangar zalunci ta haramatacciyar kasar Isra'ila da killace Palasdinawa cikin yunwa da duhu hali ne. Kuma wannan fatawa ta daurewa mutane kai da nuna takaici musamman ma ganin halin da al'ummar Palasdinu ke ciki na takurawa da kuncin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta sanya su a ciki da hatta wadanda ba musulmi ba ke ciza yatsa a kai.Shi dai Dandawi ya rasu ne a kasar Saudiya a daidai lokacin yak e ziyara a kasar inda ya fuskanci bugon zucciya a kan hanyarsa ta komawa kasar Masar.
551590