Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; it ace kasa ta hudu a duniya wajen yawan jama'a kuma tafi yawan musulmi a a duniya ta inda yawan al'ummar kasar sun zarta miliyon dari biyu da talatin da takwas kuma kaso tisi'in na al'ummar wannan kasa musulmi ne sauran kuma na bin addinan Hindu,kiristanci da budanci kuma yaren gwamnatin kasar Indonansi ne sai sauran yarurrukan kabilun kasar.Duk da cewa tun karni na sha daya miladiya ne Musulunci ya kutsa wannan kasa inda malamai da makaranta da dama suka taka rawar gani a wannan kasa amma rashin yin magana da larabci na kawo cikas ga musulmin wannan kasa ta fuskar koyarwa ta Musulunci da karatun Kur'ani mai Girma.
556250