IQNA

Wahabiyawa Na Kokarin Kawo Shaku A Cikin Nahajul Balaga

Bangaren ilimi da nazari: wahabiyawa na kokarin kawo shaku a cikin nahajul balaga da magangann Amirul muminina (AS).
Daga birnin Qum ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; wahabiyawa na kokarin kawo shaku a cikin nahajul balaga da magangann Amirul muminina (AS).Hujjatul Islama walmuslimina Huseini Kazwini malamin Hauza Ilmiya ta birnin Qum a ranar litinin din da ya gabata sha shidda ga watan Farvardin na shekarar hijira shamsiya ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a wani zama na darasin Nahajul Balaga a haramin Hadarat Ma'asuma (S) ya yi bayani kan yadda wahabiyawa ke a yau ke kokarin kawo shaku da shubuha a maganganun Imam Ali (AS) a cikin littafin nahajul balaga a hudubobinsa dari biyu da ashirin da takwas.

558496