Bangaren kasa da kasa; a kasar Malaishiya ne aka gudanar da taron share fage na kasashen musulmi kuma an gudanar da wannan taro ne a birnin Kwalalanpur fadar mulkin kasar Malaishiya.
Daga reshenta da ke kudu maso gabacin Asiya ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Muhit ta watsa rahoton cewa; a kasar Malaishiya ne aka gudanar da taron share fage na kasashen musulmi kuma an gudanar da wannan taro ne a birnin Kwalalanpur fadar mulkin kasar Malaishiya. Wannan shi ne taron ministocin ilimi mai zurfi na kasashen musulmi da ke mamba a kungiyar hadin kan kasashen musulmi OCI KO OAC kuma an samu halartar masana da jami'a da wakilan kasashen musulmi a wajen wannan taro.
558312