IQNA

Masu Ra'ayin Addini A Jodan Sun Nuna Adawa Da Raba Fim Din Kamar Musulunci A Makarantu Daga Amerika

Bangaren al'adu da fasaha: Dubban musulmai ne a kasar Jodan suna yi Allah wadai da adawa da yadda amerika ke rarra fina-finai masu nuna kama ga Musulunci a makarantun gwamnatin wannan kasa.
Daga Jodan ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar Al'ayam ta kasar Palsdinu ta watsa rahoton cewa; Dubban musulmai ne a kasar Jodan suna yi Allah wadai da adawa da yadda amerika ke rarra fina-finai masu nuna kama ga Musulunci a makarantun gwamnatin wannan kasa. Wannan dai wani sabon salon makirci ne da Amerika ta bullo da shi na yakar Musulunci da nuna adawarta da duk wani abu day a shafi Musulunci a fili karara ba tare da wani shayi na irin martanin da musulmi za su iya mayar mata da shi kan wannan lamari.


560034