Daga reshenta da ke Jodan ne bayan ta nakalto daga jaridar Alrayi da ke fitowa a wannan kasa ta Jodan ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; mabiya addini na bai daya a yankin gabas ta tsakiya sun gudanar da taro a babban birnin kasar Jodan Oman inda aka samu halartar Kiristoci na Protastan da ke Jodan. A wannan taro an samu halartar masana da kwararru musulmi da kiristoci inda suka tattauna ci gaban da addinai ke samu ta fuskoki daban daban na rayuwa da zamantakewa da akida da tattalin arziki da tsaro da dai sauransu da kuma irin matsalolin da suke fuskanta a yankin gabas ta tsakiya musamman a Kudus.
561461