IQNA

Za A Yi Bincike Kan Hadarorin Da Ke Fuskantar Kwararru Kan Koyarwa A Duniyar Musulmi

Bangaren kasa da kasa: taro kan binciken irin hadarorin da ke fuskantar kwararru kan ilimi a duniyara musulmi da za a gudanar a ranar biyu ga watan Ordebehesh na wannan shekara ta hijira shamsiya a jami'ar Alkahira.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Isesco.org ta watsa rahoton cewa; taro kan binciken irin hadarorin da ke fuskantar kwararru kan ilimi a duniyara musulmi da za a gudanar a ranar biyu ga watan Ordebehesh na wannan shekara ta hijira shamsiya a jami'ar Alkahira.
Wannan taro hukumar da ke kula da harkokin ilimi ta kungiyar hadin kan kasashen Musulunci da kuma hukumar da ke kula da ilimi da al'adu Unesko ta majalisar dinkin duniya da kuma hadin guiwar jami'o'in Musulunci da kuma jami'ar alkahira suka shirya.

566455