IQNA

Taron Kowa Da Kowa Na Kungiyar Hadin Kan Jami'o'in Duniyar Musulmi A Baku

Bangaren kasa da kasa:a ranar alhamis din da ta gabata ce aka gudanar da taron kowa da kowa na kungiyar hadin kan jami'o'in kasashen musuylmi FUMI a babban birnin kasar Azarbeijan Baku.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar ISESCO ta watsa rahoton cewa: a ranar alhamis din da ta gabata ce aka gudanar da taron kowa da kowa na kungiyar hadin kan jami'o'in kasashen musuylmi FUMI a babban birnin kasar Azarbeijan Baku. Wannan taro ya shafi kasashe hamsin da bakwai da ke cikin kungiyar kasashen musulmi da kuma aka ba wa duk wata jami'a da ke a cikin wadannan kasashe damar halartar wannan taro domin baje kolin irin matsalolin da kasashen musulmi ke fuskanta da kuma hanyoyin bi domin magance su cikin sauri da inganta lamarin.

578982